Real Madrid ta lashe kofi karo na 10
Real Madrid ta lashe kofin gasar zakarun Turai karo na 10 bayan ta samu sa’a akan Atletico Madrid a karawar karshe da suka fafata a birnin Lisbon. Sergio Ramos ne ya kwaci Real Madrid a hannun Atletico inda saura kiris a kammala wasan ya barke kwallon da Atletico ta fara jefawa a raga.
Wallafawa ranar:
Gareth Bale da Marcelo da Cristiano Ronaldo suka jefa wa Real Madrid kwallaye a ragar Atletico a cikin lokuttan da aka kara a wasan inda aka tashi ci 4-1.
Magoya bayan kungiyar Real Madrid sun gudanar da biki a birnin Madrid a jiya Lahadi domin murnar lashe kofin zakarun Turai karo na 10.
Dubun dubatar magoya bayan Real Madrid ne suka tarbi tawagar ‘Yan wasan a lokacin da suka iso a wani dandalin da kungiyar ke gudanar da biki.
Rabon da Real ta lashe kofin Zakarun Turai tun a 2002 a lokacin da ta lashe kofin karo na 9. Atletico Madrid kuma ta nemi lashe kofin ne a karon farko
Daukacin Jaridun Spain sun jinjinawa Real Madrid na lashe babban kofin na Turai karo na 10 tare da jaje da kuma yin sharhi a game da yadda makomar Atletico Madrid ta kasance a wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu