Atletico ta lashe La liga
Kungiyar Atletico Madrid ta lashe kofin La liga karo na farko tsawon shekaru 18 bayan an ta shi wasa kunnen doki a gidan Barcelona a fafatawar karshe a gasar. A bana Barcelona an watse kaka ne ba tare da ta lashe kofi ba, yayin da kuma aka an zubar da Osasuna da Valladolid da Real Betis a La liga.
Wallafawa ranar:
A birnin Madrid magoya bayan kungiyar Atletico Madrid sun gudanar da gagarumin biki a karshen mako, inda dubban magoya bayan kungiyar sanye da riga mai kalar Ja da fari suka bazama saman titi a daren Assabar da Lahadi suna bikin lashe kofin La liga.
Wannan ne karo na 10 da kungiyar ta lashe kofin La Liga a Spain.
Diego Simeone, shi ne ya sauya Atletico Madrid wanda ya akrbi aikin horar da kungiyar a 2011, a lokacin tana kasan teburin La liga.
Kafin daukar Diego Simeone a matsayin kocin Atletico akwai ‘yan wasa da dama da suka fice kungiyar da suka hada da Fernando Torres da Sergio Aguero da Diego Forlan.
Amma a zamanin Simeone, kungiyar ta lashe kofin Europa league da Super Cup na Turai da kofin Copa del Ray da La liga. Kuma yanzu kungiyar tana harin lashe kofin Zakarun Turai a karshen mako idan ta doke abokiyar hammayarta Real Madrid a birnin Lisbon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu