Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Karawar Atletico da Real Madrid

A ranar Assabar a Birnin Lisbon na Portugal za’a yi karawar karshe a gasar zakarun Turai tsakanin ‘Yan gari guda Real Madrid da Atletico Madrid. Karawar kungiyoyin biyu na nuna garin Madrid a Spain zai dare gida biyu, inda Real Madrid ke harin lashe kofin a karo na 10, yayin da kuma Atletico ke harin lashe kofin a karon farko a tarihinta.

Harabar filin wasan Sporting Lisbon da za a yi karawar karshe a gasar zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid.
Harabar filin wasan Sporting Lisbon da za a yi karawar karshe a gasar zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Amma dukkanin kungiyoyin biyu suna fuskantar matsala ta wasu Zaratan ‘Yan wasansu wadanda babu tabbas ko zasu haska a karawar mai dimbin tarihi, saboda rauni da suke fama da shi.

Tuni kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti yace Cristiano Ronaldo da Gareth bale sun murmure, amma yanzu akwai Pepe da Benzema da babu tabbas akansu.

Atelico kuma tana fatar Diego Costa masanin raga a kungiyar zai wartsake wanda ke fama da rauni, domin a ranar da suka lashe kofin La liga a karawa da Barcelona, Dan wasan ya fice fili saboda rauni.

Ramos yace ganin irin rawar da Atletico ta taka a bana, suna iya ba Real Madrid matsala, amma Ronaldo yace a gidan shi Portugal za’a yi karawar karshe, don haka za su yi kokarin lashe kofin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.