Isa ga babban shafi
Spain

Messi ya karrama Vilanova

A yau Litinin ne za’a yi bikin Jana’izar tsohon Kocin Barcelona Tito Vilanova wanda ya mutu a sanadiyar cutar kansa a makon jiya. Lionel Messi wanda ya kwaci Barcelona a hannun Villarreal a wasannin La liga a karshen mako, ya sadaukar da kwallon da ya zira a raga ga tsohon kocin shi inda aka tashi wasan ci 3-2.

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi
Dan wasan Barcelona, Lionel Messi REUTERS/Paul Hanna
Talla

A ranar Juma’a ne Vilanova ya mutu bayan shafe sama da shekaru biyu yana fama da cutar kansa.

Atletico Madrid dai na ci gaba da lashe wasanninta domin a jiya lahadi ta doke Valencia ci 1 da 0, inda ta ke harin lashe kofin La liga a karon farko tsawon shekaru 18 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.