Isa ga babban shafi
Spain

Clasico: Real Madrid ta lashe Copa del Ray

Dubun dubatar magoya bayan kungiyar Real Madrid ne suka tarbi tawagar ‘Yan wasan kungiyar a birnin Madrid da suka fito daga Valencia inda suka lashe kofin Copa Del Ray bayan sun doke Barcelona ci 2-1 a wasan karshe.

Jagoran Real Madrid Iker Casillas ya daga kofin Sarki da suka lashe bayan sun doke Barcelona
Jagoran Real Madrid Iker Casillas ya daga kofin Sarki da suka lashe bayan sun doke Barcelona REUTERS/Juan Medina
Talla

Magoya bayan kungiyar sun fito ne sanye da tutar Real Madrid domin karrama ‘Yan wasan da suka lashe kofin da Atletico Madrid ta haramta masu a bara.

Cristiano Ronaldo da Fabio Coentrao da Pepe suna murnan lashe kofi
Cristiano Ronaldo da Fabio Coentrao da Pepe suna murnan lashe kofi REUTERS/Sergio Perez

Ana saura minti 5 lokacin wasan ya cika tsadadden dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ya yi wata fitar bera da gudu ya jefa kwallo ta biyu a ragar Barcelona, bayan ana kunnen doki.

Wannan ne karo na 19 da Real Madrid ke lashe kofin na gida.

Gareth Bale shi ne ya mamaye kanun labaran Jaridun Spain, kamar yadda Jaridar Daily El Mundo ta buga babban labarinta mai taken “Kofin Bale”, yayin da kuma Jaridar El Pais ta maka hoton Casillas ya daga kofin tare da taken “Kwazon Bale ya tantance makomar kofi”.

Dan wasan Real Madrid Gareth Bale yana murna tare da Xabi Alonso
Dan wasan Real Madrid Gareth Bale yana murna tare da Xabi Alonso REUTERS/Albert Gea

Barcelona a bana ga alamu za’a watse kaka ne ba tare da ta lashe kofi ba a karon farko tsawon shekaru 6 domin an yi waje da ita a zakarun Turai kuma akwai tazara tsakaninta da Atletico a teburin La liga.

Sau uku ke nan a jere da Barcelona ke shan kashi bayan ta sha kashi Zakarun Turai, da La liga da kuma daren jiya da Real ta doke ta a Valencia.

Lionel Messi na Barcelona cikin juyayi tare da  Xavi Hernandez
Lionel Messi na Barcelona cikin juyayi tare da Xavi Hernandez REUTERS/Albert Gea

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.