Isa ga babban shafi
Premier League

Za’a dauki lokacin kafin in gina United-Moyes

Manchester City ta sake lallasa Manchester United ci 3-1 a filin wasa na Old Trafford a premier league ta Ingila wanda ya ba City damar datse yawan tazarar makin da ke tsakaninta da Chelsea da ke jagorancin teburin gasar.

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney
Dan wasan Manchester United Wayne Rooney REUTERS/Phil Noble
Talla

Kocin Manchester David Moyes yace za’a kwashe lokaci kafin ya gina sabuwar United, yana mai kira ga magoya bayan kungiyar su kara hakuri, yayin da wasu daga cikinsu suka fara caccakar Ferguson akan shi ya zabar wa United makoma marar kyau, saboda shi ne ya kawo Moyes bayan ya yi ritaya.

Yanzu tazarar maki 12 ne Chelsea ta ba Manchester United da ke a matsayi na 7, kuma yana da wahala Manchester ta tsallake zuwa gasar zakarun Turai a bana idan dai ba ta lashe kofin gasar bana wanda hakan yana da wahala domin zata kara ne da Bayern Munich mai rike da kofin gasar a zagayen Kwata Fainal.

A daya bangaren kuma, Swansea City ta rike Arsenal ne ci 2-2 a filin wasa na Emirate, Kuma bayan kammala wasan Arsene Wenger yace yanzu kan kofin Premier ya fara yi ma shi nisa domin sun yi watsi da damarsu

Tazarar maki 6 ne Chelsea ta ba Arsenal, kuma saura wasanni 7 a kammala wasannin gasar a bana.

Arsenal dai ta nemi farfadowa ne daga kashin da ta sha a hannun Chelsea ci 6-0, inda Lukas Podolski da Olivier Giroud suka sa kungiyar a kan hanya bayan Swansea ta jefa kwallo daya a ragarsu amma daga karshe Mathieu Flamini ya yi watsi da damar, bayan ya ci kansu ana mintinan karshe.

Yanzu babban kalubalen da ke gaban Arsenal shi ne haduwarta da Manchester City a karshen mako.

A yau Laraba ne Liverpool da ke harin lashe kofin Premier a bana zata kara da Sunderland tare da fatar datse yawan makin da ke tsakaninta da Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.