Isa ga babban shafi

Mutane da dama sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Switzerland

Wani jirgin ‘yan yawon bude ido ya yi hadari a wani yanki mai tsaunuka a yammacin kasar Switzerland a yau Asabar, ana fargaban mutane da dama sun mutu.

Hoto don misali...
Hoto don misali... © Rohit Giri/Reuters
Talla

'Yan sandan yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce jirgin ya yi hatsari ne a kusa da Ponts-De-Martel da ke yankin Neuchatel, toh sai dai ba su yi karin bayani ba.

Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce mutane da dama ne suka mutu a hatsarin.

‘Yan sandan sun sanar da cewa ba za su yi karin bayani game da adadin mutanen da ke jirgin ko suka hallaka ko kuma jikkata a jirgin ba har sai an sanar da iyalansu abin da ya faru.

Tuni dai ma’aikatan ceto da ‘yan sanda suka isa inda lamarin ya faru, yayin da aka fara binciken gano musabbabin hatsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.