Isa ga babban shafi

Wata ‘yar kasar Switzerland ta gurfana a gaban kuliya saboda ta'addanci

Wata ‘yar kasar Switzerland ‘yar shekara 29 da ke fama da matsalar tabin hankali ta bayyana gaban alkalai a wannan makon a Bellinzona (Switzerland) saboda “aikin ta’addanci”, a wani  kokarin yanke makogwaron wasu mata biyu a lokacin da take shelanta goyon bayan kungiyar IS a wani shagon sayar da kayayyaki a shekara ta 2020.

Kungiyar ISIL dake da'awar jihadi ta kaddamar da munanan hare hare a Turai.
Kungiyar ISIL dake da'awar jihadi ta kaddamar da munanan hare hare a Turai. © RFI
Talla

Daya daga cikin mutanen biyun ya samu munanan raunuka a wuyansa. Na biyun, wanda ya jikkata a hannu, ya yi nasarar shawo kan maharin tare da wasu mutane, har zuwa lokacin da ‘yan sandan suka iso.

A yayin harin, ta yi ta kururuwar "Allahu Akbar" da "Zan rama wa Annabi Muhammad", ta kuma bayyana tare da nuna goyon baya ga kungiyar IS mai da'awar jihadi.

Kotun Bellinzona a kasar Switzerland
Kotun Bellinzona a kasar Switzerland AFP/Archivos

Mahaifinta dan kasar Switzerland ,bangaren uwa  ‘yar asalin kasar Serbia, wacce ta kai harin ta musulunta kamar yadda  wata jaridar ta kasar  ta ruwaito.

Masu bincinke sun gano cewa yin soyayya" a shafukan sada zumunta a cikin 2017 tare daya daga cikin mayakan jihadi a Sirya  na daga cikin ababen da suka tuzzura wannan mace zuwa ga shiga wannan aiaki,banda haka sun gano cewa  ta yi ƙoƙarin shiga Syria, an kama ta a kan iyakar Turkiyya da Syria kuma aka mayar da ita Switzerland sannan aka sanya ta a cibiyar kula da masu tabin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.