Isa ga babban shafi

NATO ta soki Rasha kan barazanar jibge makaman nukiliya a Belarus

Kungiyar tsaro ta NATO ta caccaki sanarwar da Rasha ta yi a game da jibge kwarya-kwarya makaman nukiliya a Belarus don ci gaba da yakin da ta ke da Ukraine, ta na mai bayyana hakan a matsayin rashin tunani.

Kakakin kungiyar NATO Oana Lungescu.
Kakakin kungiyar NATO Oana Lungescu. REUTERS/Thierry Roge
Talla

Sai dai kakakin NATO,  Oana Lungescu ta ce kawancen na Turai bai ga wani sauyi a game da harkokin nukiliyar Rasha da zai tilasta daukar mataki daga bangaren sa ba, ta na mai cewa NATO na sa ido don samun fahimtar take-taken Rasha a game da wannan batu.

Ta ce sau da dama Rasha ta saba na ta bangaren na yarjejeniyar kayyade makamai, inda a kwanan nan ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar kayyade manyan makamai masu hatsari ta START.

A nata bangaren, Tarayyar Turaai ta bakin jagoran diflomasiyyarta, Josep Borrell ta yi barazanar kakaba wa Belarus karin takunkumai idan har ta bari Rasha ta yi amfani da yankinta wajen jibge wadannan makaman nukiliya, matakin da ya bayyana a matsayin barazana ga tsaron Turai.

Ita ko Ukraine kira ta yi da a yi zaman gaggawa a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don tattauna shirin Rasha na aikewa da kwarya-kwaryar makamin nukiliya makwafciyarta Belarus, tana mai cewa tilasta Belarus din Rasha ke yi a kan wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.