Shugaban China na ziyara a Rasha domin karfafa alaka da Putin
Shugaban China Xi Jinping ya sauka a Moscow babban birnin Rasha, ziyara ta farko da ya kai kasar tun bayan yakin da ta kaddamar akan makwafciyarta Ukraine.
Wallafawa ranar:
Yayin ganawa da manema labarai shugaba Xi ya bayyana fatan ganin ziyarar ta karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasar ta as da Rasha, wadda ya bayyana a matsayin babbar kawa.
Tun bayan barkewar yakin Rasha da Ukraine, China ta zabi zama ‘yar ba ruwanmu akai, duk da irin matsin lambar da kasashen yammacin Turai da Amurka ke yi mata, kan ta mara musu baya wajen ladaftar da shugaba Vladimir Putin.
A ‘yan kwanakin nan ne dai Amurka ta zargi kasar ta Sin da shirin bai wa Rasha taimakon makamai, zargin da China ta musanta.
Ziyarar kwanaki uku da shugaba Xi Jinping ya fara a Rasha ta zo ne kwanaki kalilan bayan da kotun duniya ICC ta bayar da sammacin kamo mata shugaba Vladimir Putin, bisa zarginsa da aikata laifukan yaki da kuma tilasta wa kananan yaran kasar Ukraine zuwa Rasha ko kuma yankunan da sojojin kasar suka mamaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu