Isa ga babban shafi

Birtaniya ta yi watsi da bukatar shugaban Scotland

Firaminisan Birtaniya Rishik Sunak ya yi watsi da bukatar sabon shugaban jam’iyyar National Party ta Scotland ta gudanar da zaben raba gardama domin samun ‘yancin cin gashin kai.

Humza Yousaf
Humza Yousaf AFP - ANDY BUCHANAN
Talla

Duk da cewa, Firaministan na Birtaniya ya yi watsi da bukatar, amma ya ce, a shirye yake ya yi aiki tare da sabon shugaban jam’iyyar ta National Party a Scotland, Humza Yousaf kamar yadda mai magana da yawunsa ya sanar.

Mai magana da yawun Firaministan ya shaida wa manema labarai cewa, al’ummar Scotland da daukacin mutanen Birtaniya sun mayar da hankali ne kan lamurran da suka fi ci musu tuwo a kwarya kamar rage tashin farashin  kayayyaki da magance tsadar rayuwa da kuma tunkarar matsalolin majinyata a asibiti.

A jiya Litinin ne Yousaf ya lashe kujerar shugabancin Scotland kuma shi ne mutun na farko mafi karancin shekaru, sannan daga wata kabila mara rinjaye da ya dare kan wannan mukamin.

Yanzu haka an zura masa ido don ganin irin rawar da zai taka wajen farfado da fafutukar neman ‘yancin Scotland daga Birtaniya bayan kawo karshen dadadden  wa’adin Nicola Sturgeon, wadda ta yi murabus a watan jiya.

Yousaf dai ya samu kashi 52 na kuri’un da mambobin jam’iyyar National Party suka kada bayan rarrabuwar kawunan da aka samu a tsakaninsu.

Za a rantsar da shi a matsayin baban minista a ranar Laraba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.