Isa ga babban shafi
Scotland- Turai

Sturgeon za ta ziyarci Brussels saboda manufar Scotland

Babbar ministar Scotland Nicola Sturgeon ta ce yau za ta je Brussels don bayyana aniyar yankin na ci gaba da zama cikin kungiyar kasashen Turai bayan kuri’ar janyewa da Birtaniya ta kada a makon jiya.

Babbar Ministar Scotland Nicola Sturgeon
Babbar Ministar Scotland Nicola Sturgeon Andy Buchanan / AFP
Talla

Sturgeon ta ce a shirye take ta kare martabar Scotland bayan ta bukaci gudanar da zaman majalisa na musamman don ba ta goyan bayan zuwa tattaunawa da kungiyar kasashen Turai.

Kashi 62 na masu zabe daga Scotland sun zabi ci gaba da zama cikin kungiyar kasashen Turai.

A bangare guda, magajin garin birnin London Sadiq Khan yaki amince wa da bukatar ballewa daga Birtaniya da wasu ke kira akai bayan zaben raba gardamar da ya tabbatar da ficewar kasar daga cikin kungiyar kasashen Turai.

Sai dai magajin garin ya bukaci bai wa birnin kujera ta musamman a tattaunawar da za a yi tsakanin Birtaniya da wakilan kungiyar kasashen Turai.

Khan ya kuma bukaci bai wa London karin karfin gudanar da ayyuka da suka hada da kashe kudade.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.