Isa ga babban shafi

Faransa da Australia sun gyara alakarsu bayan rikicin kwangilar jiragen yaki

Firaministan Australia Anthony Albanese ya yi maraba da sabuwar dangantakar kasar da Faransa, a wata ganawarsa da shugaba Emmanuel Macron yau juma'a a birnin Paris, ganawar da ke zuwa bayan takaddama kan kwangilar kera jiragen ruwan yaki da kasar ta mayar hannun Amurka da Birtaniya duk da faro batun ta da Faransar. 

Shugaba Emmanuel Macron tare da Firaministan Australia Anthony Albanese.
Shugaba Emmanuel Macron tare da Firaministan Australia Anthony Albanese. AP - Thomas Padilla
Talla

Wata sanarwar bayan ganawar shugabannin biyu a fadar Elysee ta tabbatar da sulhuntawa tsakanin kasashen na Faransa da Australia wadanda huldarsu ta samu tawaya tun bayan gushewar tsohon Firaminista Scott Morrison wanda ya karkatar da kwangilar jiragen yakin da suka kulla.

Tun farko shugaba Emmanuel Macron ya fusata ne da yadda Marrison ya karkatar da kwangilar ta dala biliyan 60 zuwa ga kasashen Amurka da Birtaniya a bara duk da cewa ya faro tattaunawa kan kwangilar da Faransa.

A wancan lokaci ne dai Faransa ta sanar da katse huldar diflomasiyya da Australia bayan da shugaba Macron ya zargi Morrison da sharara masa karya yayin liyafar cin abincin dare da suka yi a Paris cikin watan Yunin 2021.

A cewar Firaminista Albanese tun farko kamfanin kera jiragen ruwan yakin na Faransa ya amince da cinikayyar ta yuro miliyan 555 tsakaninsa da Australia gabanin samun barakar da ta kai ga katsewar kwangilar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.