Isa ga babban shafi

Autralia za ta biya Faransa diyya bayan warware cinikin jiragen ruwa

A yau asabar kasar Australia ta cimma yarjejeniya tsakanin ta da katafaren kamfanin  kera jiragen yaki na ruwa da aka sani Naval Group na  Faransa na biyan wasu kudade a matsayin diyya bayan rusa wani kasaitacen ciniki tsakanin kasashen biyu a watan satumba na shekara ta 2021.

Kamfanin kera jiragen ruwan yaki na Naval Groupe a Faransa
Kamfanin kera jiragen ruwan yaki na Naval Groupe a Faransa © Naval Group / AFP
Talla

Firaminista na wancan lokaci  Scott Morrison ne ya sanar da wannan mataki tareda bayyana  sauyin kasar ta Australia na sake cinikin wadanan jirage da Amurka da Birtaniya,alamrin da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya danganta da ci amana.

Macron da Biden sun bukaci kwantar da hankali

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaran sa na Faransa Emmanuel Macron sun amince su jingine takaddamar dake tsakanin su dangane da kwangilar ginawa Australia jiragen yakin karkashin teku, yayin da suka sha alwashin bunkasa dangantakar dake tsakanin su.

Sabon Firaministan kasar na yanzu Anthony Albanese ya amsa cewa kasar sa za ta zubawa Faransa wadanan kudade a matsayin diyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.