An gano bankunan Switzerland da ke ci gaba da boye kudaden sata
Banki na biyu mafi girma a kasar Switzerland na ci gaba da fuskantar zargin cin hanci da rashawa da kuma boye kudaden sata da na Haramun daga kasashen duniya tsahon shekaru.
Wallafawa ranar:
Wata kungiyar kasa da kasa da ke bincike kan hada-hadar kudade ce ta bankado almundahanar, inda ta ce binciken nata ya nuna yadda bankin ke da hannu dumu-dumu a boye kudaden sata daga hannun manyan ‘yan siyasar kasashen duniya.
A cewar kungiyar abin takaicin shine yadda bankin ke karbar irin wadannan kudade da cikakken sanin ta yadda aka samo su, ba kuma tare da gargadi ko horon wadanda suka kawo ba, abin da ke zama wata hanya ta goya wa masu wawushe kudin al’umma baya.
Sai dai tuni bankin mai suna Credit Suisse ya yi watsi da zargin, Inda ya ce zarge-zargen da kungiyar ta yi an yiwa bankin su ne tun shekaru 1940, kuma tuni aka magance wannan matsala.
A cewar bankin tun wancan lokaci ne kuma aka fara rufe asusun irin waddannan mutane, yayin da aka karkare aikin a 2015, abinda ke nufin a yanzu babu asusun irin wadannan mutane a bankin.
To sai dai kungiyar wadda ta samu hadin kan wasu manyan kafafen yada labarai na duniya wajen kaddamar da binciken ta tsaya kai da fata kan cewa har kwanan gobe ana irin wannan mummunan aiki a bankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu