Switzerland za ta mayar wa Najeriya Dala miliyan 321
Gwamnatin Najeriya ta ce, kasar Switzerland na shirin maido ma ta da Dala miliyan 321 da ake zargin marigayin tsohon shugaban kasar a mulkin soja, Janar Sani Abacha da wawushewa daga asusun gwamnati.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan Shari’a na Najeriya ta ce, matakin maido da kudin ya biyo bayan cimma wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin Najeriya da Switzerland da bankin duniya.
Yarjejeniyar wadda bangarorin suka sanya wa hannu a Zurich, ta bayyana tsare-tsaren da za a yi amfani da su wajen maido da makuden kudaden cikin Najeriya.
Bayanai na cewa, an fara dakile kudaden ne a Luxembourg kafin daga bisani gwamnatin Switzerland ta kwace a shekarar 2014 bayan ofishin masu shigar da kara da ke Geneva ya gabatar da korafi akan kudin.
Kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ce, Marigayi Janar Sani Abacha ya wawushe Dala biliyan 5 daga asusun Najeriya a cikin shekaru biyar da ya jagoranci kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu