Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Lafiya Jari Ce : Cutar kyandar biri na ci gaba da zama barazana
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan yadda cutar kyandar biri ke ci gaba da zama baraza sakamakon yaduwarta a kasashen duniya da dama ciki harda Najeriya, inda ta kama sama da mutane dubu biyu a sassan jihar.06/06/202210:04 -
Lafiya Jari Ce: shawarar masana kan kariya daga cutar Sankara
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya tattaunawa kan Cutar Sankarau dake addabar al'umma a Arewacin Najeriya masamman a irin wannan lokaci da yankin ke fuskanctar tsananin zafi ko kuma farkon zubar ruwan sama, yanayin da kan haddasa bullar cutuka daban-daban kama daga Sankarau, kyanda kwalara da kuma zazzabin cizon sauro wadanda a lokuta da dama kan haddasa asarar dimbin rayuka.30/05/202210:11 -
Lafiya Jari Ce: Shawarwarin masana kan yaki da cutar yoyon fitsari
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattaunawa ne kan ranar 23 ga watan Mayun da Majalsar Dinkin Duniya ta ware amatsayin ranar yaki da cutar yoyon Fitsari da nufin kawo karshen matsalar a cikin al’umma.23/05/202210:02 -
Ta'azzarar zazzabin typhoid a jihar Nasarawa
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai duba batun barkewar cutar zazzabin typhoid a jihar Nasarawa ta arewacin Najeriya, cutar da ke cikin jerin manyan cutukan da ke janyo asarar rayuka da dama a sassan kasar. Shirin ya tattauna da kwararru a fannin kiwon lafiya, wadanda suka yi karin haske a game da cutar da kuma yadda za a kare kai daga kamuwa da wannan shu'umi zazzabi.16/05/202210:01 -
An samu karin masu fama da cutar TB a Jamhuriyar Nijar
Shiirn Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna akan karuwar masu fama da tarin TB a Jamhuriyar Nijar.11/04/202209:52 -
Illar cin abinci marar sinadaran gina jiki ga lafiyar dan adam
Shirin Lafiya jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan illar cin abinci marasa gina jiki da mutane suka dogara da shi a wannan zamani, nau'ikan abincin da ke haddasa cutuka masu alaka da zuciya ko koda ko kuma haddasa hawan jini. Ayi saurare Lafiya.28/03/202209:56 -
Yadda shaye-shaye ke shafar lafiyar kwakwalwar matasa a Najeriya
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan rana tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan karuwar matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi duk ikirarin mahukunta na yakar matsalar a matakai daban-daban, dai dai lokacin da wani binciken masana ke alakanta matsalar ta shaye-shaye da karuwar masu tabin hankalin da ake gani a sassan kasar.21/03/202210:16 -
Shan taba Sigari da dangoginta na lakume rayuka kusan miliyan 2 duk shekara
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki kan sabbin alkaluman da majalisar dinkin duniya ta fitar da suka nuna cewar mutane akalla miliyan 1 da dubu 900 ke mutuwa a sakamakon shan taba Sigari da sauran nau'ikanta.16/03/202209:34 -
Lafiya Jari Ce : Bullar cutar Sankarau a jamhuriyar Nijar
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi dubi kan bullar cutar sankarau a jamhuriyar Nijar, wanda tuni ta hallaka mutane a kasar.07/03/202209:50 -
Yadda mutane suka jahilci cutar Cancer wajen alakanta ta da aljanu
A jamhuriyyar Nijar wata cuta da ake kira matabiya ko kuma maharbiya na ci gaba da tsananta kama daga birane zuwa karkara, cutar da mutane ke alakantawa da aljanu duk da gargadin masana kiwon lafiya da ke ganin galibin makamantan cutar ko dai su kasance kurji da ka iya warkewa ko kuma Cancer a wasu lokutan amma tsoro yakan hana jama'a mika kansu ga asibiti.28/02/202209:59 -
Dambarwa tsakanin jinsin mata da maza a kan tsarin kayyade iyali
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon, yayi dubi ne a kan dabarwa a tsakanin maza da mata da ta dabaibaye batun tsarin kayyade iyali, inda aka takaita magungunan kayyade haihuwa ga mata ne kawai ba tare da an samar da na maza ba,21/02/202210:07 -
Masu harbuwa da cutar kuturta na karuwa a Najeriya
Shirin 'Lafiya Jari Ce' ya yi nazari ne kan alkalumman majalisar dinkin duniya da ke nuni da cewa masu harbuwa da cutar kuturta a Najeriya, lamarin da masana lafiya suka danganta da sakaci.14/02/202210:02 -
Dawowar cutar Polio a wasu sassan Najeriya bayan an fatattake ta
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi dubi ne kan sake bayyanar cutar shan ina, wato Polio a wasu sassan Najeriya, bayan da hukumomi suka ce an fatattake ta.28/01/202210:08 -
Zaman kotun ladabtar da likitoci don rage matsalar sakaci a bangaren lafiya
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda zaman kotun sauraron korafe-korafe kan likitoci ya gudana, a wani yunkuri da hukumar kula da ayyukan likitoci ta Najeriya ke yi don magance yawan sakacin da likitocin ke yi a bakin aiki.13/12/202110:15 -
Bayani a kan sabon nau'in cutar covid-19 na Omicron
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon, ya yi dubi ne da sabon nau'in cutar Covid-19 na Omicron da aka fara ganowa a kasar Afirka Ta Kudus. Azima Bashir Aminu ce ta shirya ta gabatar, tare da taimakon wakilinmu na Bauchi an Najeriya Ibrahim Malam Goje.06/12/202109:57
Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.