Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Magungunan da aka sarrafa daga itatuwa na samun karbuwa a tsakanin mutane
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon ya tattauna da masana akan yadda magungunan da aka sarrafa daga itatuwa da nau'ikan kayan abinci ke samun karbuwa a tsakanin mutane.29/11/202109:40 -
Red Cross ta samar da manhajar duba lafiyar kananan yara a Adamawa
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali kan wani shirin inganta lafiyar kananan yara a yankin arewa maso gabashin Najeriya bisa hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross da gwamnatin jihar Adamawa wanda ya kai ga samar da wata manhajar duba yara tare da lalubo lalurar da ke damunsu. Ayi saurare Lafiya.22/11/202110:21 -
'Yan Najeriya sama da miliyan 6 na dauke da cutar Siga (Diabetes)
Shirin 'Lafiya Jari Ce' a wannan makon ya duba batun illolin cutar sukari ko kuma diabetes a turance, cutar da bisa al’ada ake gudanar da bikin yaki da ita a kowacce ranar 14 ga watan Nuwamba a wani yunkuri na wayar da kan jama’a game da illolinta dama yadda za a kare kai daga kamuwa da ita.15/11/202110:25 -
Yadda cutar tsananin damuwa ke kisan mummuke ga miliyoyin mutane
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu na wannan mako, ya yi duba kan yadda cutar tsananin damuwa kan kisan miliyoyin mutane ba tare da sani ba, cutar da WHO ke cewa ta na barazana ga rayukan mutane musamman a nahiyar Afrika09/11/202109:47 -
Mahimmanci duba lafiya akai akai
A cikin shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako, Azima Bashir Aminu ta yi nazari ne a kan mahimmancin duba lafiya akai akai, inda masana harkar lafiya suka shawarci al'umma da su rika duba lafiyarsu akalla sau 3 a shekarar.11/10/202110:00 -
Bincike ya ce 6 daga cikin yara 10 a Najeriya ba iyayen su suka haife su ba
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu, ya tattauna kan rahoton binciken wani kwararren likita biodun Salami da yayi fice wajen gwajin kwayar halittar Bil Adama a Najeriya, wanda ya ce daga cikin yara 10 da ake gabatar musu domin yin gwaji, 6 daga cikin su ba mutanen da ake zaton iyayen su ne suka haife su ba.27/09/202110:02 -
Shawarar masana kan alfanun bada tallafin jini ga mabukata
Shirin 'Lafiya Jari ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba bayanai dake nuna yadda aka bar Najeriya da wasu kasashe masu tasowa galibi daga nahiyar Afrika a sahun baya ta fuskar bayar da tallafin jinni a asibitoci.20/09/202109:31 -
Kalubalen da masu fama da lalurar laka ke fuskanta a Najeriya
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan yadda masu fama da lalurar laka ke rayuwa da kuma kalubalen da su ke fuskanta dai dai lokacin da Duniya ke ware kowacce ranar 5 ga watan Satumba don wayar da kai kan matsalar.13/09/202110:18 -
Najeriya ta samar da sabon salon wayar da kan al’umma game da annobar Corona
Shirin wannan mako zai yada zango ne a tarayyar Najeriya inda gwamnatin kasar ta kara fidda sabon salon wayar da kan al’umma game da tabbatuwar annobar Corona, da kuma rungumar allurar rigakafin ta.Wannan ce ta sa gwamnatin ta yi hadin gwiwa da wasu da kungiyoyin mata don taka irin tasu rawar game da fatattakar cutar a kasar a wani taro da hukumar lafiya matakin farko ta shirya d kungiyar mata mai taken MUM.Rukayya Abba Kabara ce ta jagoranci shirin a yau.16/08/202110:01 -
Yadda al'umma ke kin amincewa da allurar rigakafin annobar korona
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu, ya tattauna kan yadda al'umma masamman a kasashe masu tasowa ke kin amincewa da karbar allurar rigakafin annobar korona.19/07/202110:10 -
Fargabar al'umma bayan sake bayyanar cutar Shan'inna a Najeriya
Shirin 'Lafiya Jari Ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba fagabar da al'umma a Najeriya suka shiga sakamakon sake bayyanar cutar Polio ko Shan'inna a wasu sassan kasar, shekara guda bayan da Hukumar lafiya ta Duniya ta wanke kasar daga wannan cuta.12/07/202109:59 -
Shawarar masana ga iyaye mata kan shayer da yara nonon uwa
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya maida hankali kan yadda iyaye mata ke yin sakaci wajen shayer da jariransu nonon uwa, inda suke maye gurbinsa sa nau'ukan abincin gongoni.05/07/202109:56 -
Yadda masu rike da madafun iko ke fita ketare don neman kulawar lafiya
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda majinyata daga Najeriya musamman masu rike da madafun iko kan tsallake asibitocin cikin kasar tare da balaguro wasu kasashen don duba lafiyarsu, lamarin ake dangantawa da sake tabarbarewar harkokin kula da lafiya a ilahirin asibitocin gwamnatin kasar.21/06/202110:17 -
Hukumomi na kokarin dakile cutar Cholera da ta bulla a Bauchi (2/2)
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya cigaba ne kan tattauna halin da ake ciki a jihar Bauchin Najeriya inda hukumomi ke kokarin dakile yaduwar cutar amai da gudawa ko kuma Cholera wadda aka samu bullarta a sassan Jihar.14/06/202109:51 -
Hukumomi na kokarin dakile cutar Cholera da ta bulla a Bauchi
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya zango a jihar Bauchin Najeriya inda hukumomi ke kokarin dakile yaduwar cutar amai da gudawa ko kuma Cholera wadda aka samu bullarta a sassan Jihar.07/06/202110:23
Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.