Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Illar da maganin cizon sauro ke yi wa jami'a
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan illar da maganin cizon sauro ke yi wa al'umma.21/09/202009:47 -
Yadda likitocin Yola suka raba tagwaye
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi nazari ne kan nasarar da likitocin Najeriya suka samu na raba wasu tagwaye a jihar Adamawa bayan an haifa su manne da juna tare da amfani da hanta guda.14/09/202009:52 -
Yunkurin WHO na yi wa yara rigakafin zazzabin cizon sauro a arewacin Najeriya
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya duba yunkurin d hukumar lafiya ta duniya WHO ke yi ne a game da yi wa dimbim yara a rewacin Najeriya allurar rigakafin zazzabin cizon sauro.24/08/202009:58 -
Yadda za a magance ciwon hanta
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Zainab Ibrahim ya yi nazari kan cutar hanta da ke illa ga al'ummar duniya, yayin da alkaluman hukumomi ke cewa, akalla mutane fiye da miliyan 250 ke dauke da cutar a duniya.20/08/202010:04 -
Yadda za'a taimakawa mai dauke da cutar farfadiya
Shirin Lafiya Jari Ce ta wannan mako ya yi dubi dangane da cutar Farfadiya ko Epilepsy a Turance, yadda al’umma suka kasance cikin duhu kan yadda za’a taimaka ko kawo daukin gaugawa ga wadanda ke dauke da cutar dake da hadarin gaske ga masu fama da ita.27/07/202010:07 -
Yadda yaki da coronavirus zai sabbaba karuwar mace-macen masu HIV TB da kuma Malaria
Shirin lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani rahoton kungiyar agaji ta Global Fund da ta yi hasashen karuwar cutukan HIV Aids, tarin fuka na TB da kuma zazzabin cizon sauro, sakamakon yadda hankulan duniya ya karkata wajen yaki da coronavirus.20/07/202010:12 -
Yadda coronavirus ta haddasa tsoron tsoro tsakanin Likitoci da Majinyata a Najeriya
Shirin lafiya jari ce na wannan makon ya yi duba kan halin tsoron tsoro da aka shiga tsakanin majinyata da likitoci a Asibitocin Najeriyar sanadiyyar annobar coronavirus wadda ta samu kwarmatawa daga kafafen yada labarai game da hadurranta.06/07/202010:00 -
Rashin kulawa kan iya janyo mutuwar yara kanana a cewar UNICEF
A wannan lokaci da annobar Covid 19 ke ci gaba da kisa ,hukumar UNICEF na gargadi zuwa iyayen yara na ganin sun mayar da hankali don bayar da kulawa da ta dace ga yaran su.A Najeriya,kungiyoyi da iyaye na ci gaba da kira ga hukuma don samun kayaki na zamani da jami'an kiwon lafiya da suka dace da zasu taimaka don takaita yaduwar anobar da ma wasu matsalloli da suka jibanci kiwon lafiya.Azima Aminu ta duba labarin da ya shafi asusun tallafawa yara kanana na UNICEF a cikin shirin lafiya jari ce.15/06/202009:57 -
Halin da kasashen duniya ke ciki kan yaduwar annobar Coronavirus
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya mayarda hankali ne kan nazarin halin da annobar Coronavirus ko COVID-19 ta jefa kasashe a ciki, musamman kasashe marasa karfi dake nahiyar Afrika.23/03/202009:59 -
Yawaitar likitocin bogi a Najeriya
Shirin 'Lafiya Jari ce ' na wannan mako tare da Zaina Ibrahim ya duba matsalar yawaitar likitocin bogi a Najeriya. A yi sauraro lafiya.16/03/202010:13 -
Matakan da Najeriya ke dauka don dakile annobar Coronavirus
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon yayi nazari ne kan bullar annobar murar mashako ta Coronavirus a Najeriya, da kuma irin matakan da kasar ke dauka don dakile haduwar annobar.02/03/202010:05 -
Kalubalen kula da lafiya a lokutan Hunturu
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna da kwararrun likitoci kan kalubalen kula da lafiyar jiki a lokutan sanyi ko iskar hunturu, musamman ta fuskar cutukan dake shafar hanyoyin numfashi.17/02/202010:12 -
Ranar Yaki da Cutar Kansa ta Duniya
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu, ya yi nazari ne kan yaki da cutar Kansa ko kuma Daji a daidai lokacin da aka gudanar da ranar yaki da Kansa ta Duniya.10/02/202009:54 -
Karin bayani kan annobar murar mashako ta Coronavirus
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon yayi nazari kan halin da ake ciki dangane da barkewar annobar murar mashako ta Coronavirus a China, wadda ta bazu zuwa wasu gwamman kasashe. Zalika shirin ya tattauna da kwararrun likitoci da suka yi cikakken bayani kan cutar.03/02/202010:15 -
Kalubalen da mata masu ciki su ke fuskanta a Asibitocin Najeriya
Shirin lafiya Jari ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda mata masu ciki ke fuskantar tsangwama a Asibotocin Najeriya. Ayi saurare Lafiya.09/12/201909:39
Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.