Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Yadda mutane ke boye cutuka masu nasaba da kwakwalwa
Shirin 'Lafiya Jari ce' ya mayar da haankali ne a kan yadda mutane ke boye cutukan da ke damunsu har su kai ga ta'azzara a jikinsu, musammam cutukan da suka shafi kwakwalwa. sau da damu a cikin al'ummarmu, mutane ba sa zuwa ganin likitan kwakwalwa, ko kuma kaai 'yaan uwansu, don kawai kada a danganta su da laallurar tabin hankali.31/10/202210:41 -
Kashi 50 na kananan yara a arewacin Najeriya na fama da cutar yunwa ko Tamowa
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda cutar tamowa ko kuma yunwa sakamakon rashin abincin mai gina jiki ke kashe yara miliyoyin kananan yara duk shekara inda a baya-bayan nan wasu alkaluman MSF ke nuna yadda kusan kashi 50 na yaran arewacin Najeriya ke fama da wannan cuta. Ayi saurare Lafiya.24/10/202210:57 -
Sama da kashi 67 na matan Najeriya na fama da karancin jini
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna da kwararru kan wani rahoto da ya bayyana cewar, fiye da kashi 67 na mata a Najeriya, na fama da matsalar karancin jini.17/10/202210:16 -
Kotun hukunta likitoci ta saurari kararrakin da aka shigar gabanta
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon yayi duba ne ga zaman kotun hukunta likitocin da aka shigar da kararrakinsu gabanta, sakamakon saba ka'idojin aiki.10/10/202209:55 -
Illar cutar cizon mahaukacin kare ga lafiyar dan adam
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan illar cutar cizon mahaukacin kare da aka fi sani da zangai ko kuma Rabies a turance, cutar da mutum kan dauka da zarar karen da ke fama da wata nau'in cuta ya cije shi, ko da ya ke akwai dabbobi da dama da ke haddasa kamuwa da cutar.05/10/202209:50 -
Matsalar karancin jini sakamakon zazzabin cizon sauro a Jamhuriyar Nijar
Shirin a wannan mako zai duba matsalar karancin jini ga yara da mata masu juna biyu da kamarin cutar Malaria ko zazzabin cizon sauro ke haddasawa aa jamhuriyar Nijar musaman a Jihar Maradi.26/09/202209:54 -
Makomar yaki da cutar Kuturta a Jamhuriyar Nijar
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna akan halin da ake ciki dangane da yaki da cutar Kuturta a Jamhuriyar Nijar.19/09/202209:47 -
Bayani a kan cutar idanu ta keratitis da ke barazanar makanta al'umma
A cikin wannan shirin, Azima Bashir Aminu ta yi nazari ne a kan cutar nan ta idanu da ke barazana ga al'umma. An yi kiyassin cewa a duk shekara, ana samun mutane dubu 3 da ke kamuwa da wannan cuta, wanda aka ce idan ba a kula ba tana makantarwa. Shirin ya tattauna da kwararre da kuma wadanda cutar ta addaba.12/09/202209:21 -
UNICEF ta samu nasara wajen rage yawaitar mace-macen yara a Najeriya
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi nazari ne kan nasarorin da Hukumar Kula da Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta samu a Najeriya ta rage mutuwar kananan yara da shayar da jarirai nonon uwa zalla da kuma yaki da auren wuri.05/09/202210:06 -
Abincin da ke haddasa cutar daji a jikin dan Adam
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan wasu nau'ukan abinci da ke haddasa cutar daji ko kuma Kansa a jikin dan Adam.22/08/202209:38 -
Yadda sabbin cutuka suka bazu a duniya
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne game da bullar sabbin cututtuka a duniya a daidai lokacin da ake fama da tsoffin cutuka da ke ci gaba da zama kalubale15/08/202210:00 -
Yadda farashin magunguna ya yi tsada dai dai lokacin da ake ganin bullar cutuka
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan ya mayar da hankali kan yadda ake fuskantar tsadar magunguna a asibitocin Najeriya dai dai lokacin da ake tsaka da ganin bullar cutuka daban-daban, musamman a jihar Kano ta arewacin kasar mai yawan jama'a. Ayi saurare Lafiya.08/08/202210:15 -
Illar da cutar hanta ke yi wa dan Adam
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu na wannan makon ya yi nazari ne kan matsalar cutar hanta wadda alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, tana kashe mutane akalla miliyan 1 a kowace shekara.01/08/202210:08 -
Cutar zazzabin cizon sauro na ci gaba da zama barazana ga 'yan Najeriya
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar Malaria da kuma tsanantar ta a sassan Najeriya, cutar da ke kashe mutane fiye da dubu dari 300 duk shekara galibi kananan yara da mata masu juna musamman a yankunan karkara da ake samun yawaitar sauro mai haddasa cutar.27/06/202210:18 -
Yadda cutar kyanda ta addabi kananan yara a Najeriya daga 2018
Shirin a wannan makon ya mayar da hankali kan cutar kyanda, cutar da a Najeriya alkaluma suka nuna yadda ta harbi kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 akalla dubu dubu 50 daga 2018 zuwa bara ciki har da yara kimanin dari 3 da ta kashe.20/06/202209:54
Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.