Gwamnatin Najeriya ta sake kokawa kan yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Najeriya ta sake bayyana damuwa a kan yawan yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar, wadanda ta bayyana yawansu a matsayin barazana ga zaman lafiyar yankin.
Alkaluma sun nuna cewa akalla yara dubu 680 ne basa zuwa makaranta a Jihar Kaduna, yayin da yawansu ya kai sama da dubu 500 a Jihar Gombe.
Dangane da wannan matsala da kuma barazanar da tattare da shi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abba Haladu, shugaban hukumar kula da karatun manyan mutane a Najeriya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu