Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Gwamnatin Kaduna ta gano makarantar allo dauke da yara mata

Wallafawa ranar:

Gwamnatin Jihar Kaduna dake Najeriya ta sanar da gano wata makarantar allo mai dauke da yara mata kanana wadanda shekarun su basu wuce 8 zuwa 10 ba.Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka na rufe irin wadannan makarantu da kuma mayar da almajiran inda suka fito,Rahotanni sun ce adadin yammatan da aka gano ya zarta 15 cakude da sauran almajirai maza a tsangayar da aka rufe.Dangane da wannan al’amari Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Kwamishiniyar kula da harkokin mata da jin dadin jama’a ta Jihar Kaduna Hajiya Hafsat Muhammad Baba.

Harabar cikin wata makarantar allo da horas da kangararru a Kaduna. 27/9/2019. (An yi amfani da wannan hoto domin misali kawai)
Harabar cikin wata makarantar allo da horas da kangararru a Kaduna. 27/9/2019. (An yi amfani da wannan hoto domin misali kawai) REUTERS/Afolabi Sotunde
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.