Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Yadda muka yi rayuwa a hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da mu - Dayyabu

Wallafawa ranar:

A karon farko karin fasinjojin jirgin kasa guda bakwai da 'yan bindiga suka sako a karshen makon da ya gabata bayan kwashe fiye da kwanaki  100 a tsare, sun bayyana halin da suka tsinci kansu, inda suka koka kan yadda ba sa iya ko barci domin tunawa da sauran fasinjojin da ke hannun 'yan bindigar.

Jirgin kasan da 'yan ta'adda suka kaiwa hari a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Jirgin kasan da 'yan ta'adda suka kaiwa hari a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. © Daily Trust
Talla

Muhammad Dayyabu wanda aka fara sako matarsa da ke dauke da juna biyu, na cikin wadanda aka sako, ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi duk me yiwuwa wajen ganin an sako sauran  wadanda suka rage cikin gaggawa.

Ya dai fara ne da bayyanawa wakilinmu da ke Kaduna Aminu Sani Sado halin da suka tsinci kansu a ciki bayan da aka yi garkuwa da su a cikin jirgin kasa akan hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.