Isa ga babban shafi

Sojin Nijar sun amince CFA sama da tiriliyan 2 a matsayin kasafin kudin bana

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta bayyana kasafin kudin kasar na shekarar bana a matsayin cfa tiriliyan 2 da milyan dubu  653. 

Ali Mahamane Lamine Zeine Niger
Fara ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine. AFP - -
Talla

Sanarwar da aka fitar bayan taron majalisar ministoci da aka gudanar jiya alhamis, ta yi hasashen cewa kasar za ta samu habakar tattalin arziki na akalla 7.9% a wannan shekara, yayin da albashin ma’aikata zai karu daga daga cfa bilyan 17 da milyuan 970 zuwa bilyan 363 saboda za a dibi sabbin ma’aikata bana. To anya wannan abu ne mai yiyuwa lura da cewa kasar tana karkashin takunkumai saboda juyin mulki. 

Wasu daga cikin sabbin matakai da gwamnati ke shirin dauka domin samun kudaden shiga, sun hada da haraji da kuma kara inganta yadda ake samun kudade a cikin gida da kuma yadda ake sarrafa kudaden. 

Kazalika, sanarwar gwamnati ta yi nuni da cewa za a kara tsaurara matakai domin yaki da rashawa, zamba cikin amince da kuma rage kashe kudade don daukar dawainiyar manyan jami’an gwamnati. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.