Isa ga babban shafi

Nijar za ta fara sayar da man fetur ga kasashen ketare a watan janairun badi

Jamhuriyar Nijar za ta fara cinikayyar danyen man fetur karon farko a tarihi cikin watan Janairu mai kamawa, kamar yadda jagoran gwamnatin sojin kasar Abdourahamane Tiani ya shaidawa manema labarai.

Shugaban na wadannan kalamai ne dai-dai lokacin da kasar ke ci gaba da shan matsin takunkumai da aka kakaba mata
Shugaban na wadannan kalamai ne dai-dai lokacin da kasar ke ci gaba da shan matsin takunkumai da aka kakaba mata AP
Talla

Da yake tattaunawa da gidan talabijin din kasar Mr Tchiani ya ce za’a fara amfani da babban bututun danyen man fetur da aka gina tsakanin kasar da Jamhuriyar Benin wajen fara wannan aiki.

Tun ranar 1 ga watan Nuwamban da ya gabata ne aka yi bikin kaddamar da wannan bututu da ya tashi daga yankin Agadem na Nijar zuwa birnin Kwatano.

Ya ce nan da watan Janairu, Nijar din zata cika manyan rumbunan ta dake kasar ta Benin, kafin daga bisani a fara shigar da shi kasuwannin duniya.

Ana sa ran kasar zata iya fitar da ganga dubu 90 kowacce rana, sai dai kuma kaso 25 ne zai samu damar fita ta wannan bututu.

Kasar na da wata karamar matatar mai da za’a iya tace ganga dubu 20 kowacce rana, kuma itace ke samar da man fetur din da ake amfani da shi a cikin gida.

Tchiani ya ce yanzu abinda gwamnatin sa zata mayar da hankali shine yadda za’a habbaka samar da tatacen mai a cikin gida maimakon jiran na kasashen ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.