Tattaunawa da Farfesa Khalid kan bukatar sake bude iyakar Najeriya da Nijar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:30
Malaman addinin Islama a Najeriya sun bi sahun wasu ‘yan kasar da Majalisar dokoki da ta dattawa, wajen bukatar ganin gwamnatin Najeriya ta bude iyakokin ta da Jamhuriyar Nijar domin sakin mara ga talakawan dake tsakanin kasashen biyu, sakamakon takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakabawa kasar bayan juyin mulkin soji.
Rahotanni sun ce mazauna iyakokin kasashen biyu na Najeriya da Nijar na fuskantar mawuyacin hali wajen katsewar harkokin kasuwanci da kuma na yau da kullum.
Dangane da haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Khalid Aliyu, Sakataren kungiyar Musulmin Najeriya ta JNI kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu