Majalisa ta jinkirta muhawara kan bukatar bude iyakar Najeriya da Nijar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:03
Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da muhawara akan kudurin da aka gabatar mata na bukatar sake bude iyakokin kasar da Jamhuriyar Nijar, sakamakon kuncin rayuwar da ya jefa mazauna jihohi 7 da ke makotaka da kasar, wadanda suka saba gudanar da harkokin kasuwanci a tsakaninsu.
Rufe Iyakokin ya biyo bayan kudirin kungiyar ECOWAS sakamakon juyin mulkin da sojoji suka gudanar a ranar 26 ga watan Yuli.
Sanata AbdurRahman Kawu Sumaila daga jihar Kano ne ya gabatar da kudurin, kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan batun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu