Isa ga babban shafi
RAHOTO

Takunkumin ECOWAS ya jefa al'ummar Nijar cikin matsin rayuwa

A Jamhuriya Nijar, al'ummar jihar Dosso dake kan iyaka da kasar Benin, sun fada cikin matsanancin halin tsadar rayuwa ta dalilin takun-kuman Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO wadanda aka laftawa kasar sakamakon juyin mulkin soji. 

Magoya bayan gwamnatin sojin Nijar kenan, lokacin da suke zanga-zangar neman ficewar sojin Faransa daga kasar.
Magoya bayan gwamnatin sojin Nijar kenan, lokacin da suke zanga-zangar neman ficewar sojin Faransa daga kasar. AFP - -
Talla

Tattalin arzikin wannan yankin ya raunana sosai, yayin da harkar Jigilar fasinjoji tsananin yankin da kasar Bénin ya tsaya ciki.

Kasar dai ta fada cikin wani yanayi na matsin rayuwa, tun bayan da sojoji suka kwace mulki daga hannun farar hula, abin da ya sanya aka kakaba mata takunkumin tattalin arziki.

Nijar dai na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da matsalar mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Zainab Ibrahim.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.