Isa ga babban shafi

Nijar ba ta zama saniyar ware ba - Firaminista Ali Lamine Zeine

Firaministan jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine, ya wakilci kasar a taron hadin gwiwa tsakanin Saudiyya da Afirka wanda ya gudana a birnin Riyad ranar 10 ga wannan wata, inda ya rattaba hannu da Saudiyya kan wata yarjejeniya domin habaka ilimi a Nijar.

Ali Mahamane Lamine Zeine Niger
Firaministan jamhuriyar Nijar Ali Lemine Zeine, yayin jawabi ta gidan radiyo da talabijin na kasar.4/9/23 AFP - -
Talla

Da yake jawabi a gidan Radiyo da Talabijin din kasar, Franminista da gwamnatin soji ta CNSP ta nada Ali Mahmane Lamine Zeine ya ce, halartan taron da Nijar ta yi a kasar Saudiyya, na tabbatar da cewa kasarsa ba ta zama saniyar ware ba.

Wannan dai shine karon farko da Nijar ta samu goron gayyatar manyan taruka, tun bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli, wanda kungiyoyin yankin suka dakatar da ita daga cikinsu har sai an maido da hambarerren shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta kakaba mata takunkumi.

A cewar Abdou Dan Neito mai fafutukar kare hakkin dan adam, gayyatar Nijar domin halartar wannan taro, wani sako ne da ke tabbatar da cewa ba wai duk duniya ce take adamawa da juyin mulkin da ake yi a kasar ba.

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren abin da Abdou Dan Neito ke cewa: 

Abdou Dan Neito na kungiyar farar hula a jamhuriyar Nijar
00:59

Abdou Dan Neito na kungiyar farar hula a jamhuriya Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.