Isa ga babban shafi

Nijar ta nemi Togo ta shiga tsakaninta da kasashen duniya

Wata tawagar gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta kai ziyara Togo tare da ganawa da shugaban kasar Faure Gnassingbe a daidai lokacin da Togo ta ce a shirye take ta sasanta tsakanin sojojin na Nijar da kungiyar ECOWAS.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar © Stringer / Reuters
Talla

Janar Salifou Mody, Ministan Tsaron Nijar wanda kuma ya jagoranci tawagar, ya ce sun kai ziyarar ce domin yi wa mahukuntan Togo bayani a game da halin da ake ciki a Nijar. 

Ministan ya ce babbar bukatarsu ita ce janyewar illahirin dakarun Faransa daga Nijar kamar dai yadda aka kulla yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu. 

A cikin wannan yarjejeniya, mun bukaci ganin an bai wa wasu kasashe damar kasancewa shaida. Mun bukaci Amurka wadda ke da dimbin sojoji a kasar domin ta kasance shaida, sannan mun bukaci a bai wa ‘yar uwarmu Togo, wadda ke taka muhimmiyar rawa saboda ta kasance kasar da za ta tsaya a madadinmu don kare wannan yarjejeniya. Inji Ministan.

A halin yanzu dai Faransa na ci gaba da janye dakarunta, kuma jiragen saman yakinta na daf da barin kasar ta Nijar. 

Sai dai Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey ya yi kakkausar suka a game da kwace mulki da karfi da sojoji suka yi a Nijar, amma ya ce a shirya suke domin yin aiki da sojojin. 

Ina mai godiya saboda yadda kuka nada Togo domin kasancewa tare da Amurka a matsayin wadanda za su kasance shaida daga farko har zuwa karshen janyewar dakarun Faransa daga Nijar. Ina mai godiya da yadda kuka nuna mana cewa lalle kuna cikin shirin yin aiki da sauran kasashe domin samun nasarar rikon kwarya a Nijar. 

Togo dai ta ce tana shirye domin shiga tsakanin sojojin Nijar da kuma sauran kasashen duniya ciki kuwa har da ECOWAS wadda ta kakaba wa kasar takunkumai ciki har da na kasuwanci. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.