Tiani ya yi alkawarin gabatar da jawadalin mika mulki ga farar hula
Jagoran gwamnatin sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, ya ce a cikin wannan mako, zai bayyana wa al’ummar kasar jadawali dangane da yadda za a gudanar da zabuka da kuma mika mulki ga fararar hula.
Wallafawa ranar:
Janar Abdourahman Tiani, wanda ya bayyana haka yayin gabatar da jawabi a game da zagayowar ranar Jamhuriya, ya yi amfani da kakkausan harshe wajen sukar matakan da kungiyar Ecowas ta dauka kan Nijar, yayin da a hannu daya ya bayyana alfahari da matakin da suka dauka na soke wasu yarjejeniyoyi da ke tsakanin Nijar da Faransa.
Jawabin shugaban gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani
A ranar Juma'ar da ta gabata kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta amince da cewar an yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, bayan tabbatar da hakan a hukumance ne kuma, ECOWAS din ta dakatar da kasar daga cikinta har sai lokacin da aka mayar da kundin tsarin mulki.
Takunkuman da ECOWAS ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar dai na ci gaba da yin tasiri a bangarori da dama, musamman akan harkokin kasuwanci inda dubban 'yan kasuwa a ciki da makwaftan kasar suka tafka hasarar kayayyakinsu da suka makale akan iyaka, sakamakon matakin ladaftarwar da hukumomin kasa da kasa suka dauka kan sojojin da suka yi juyin mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu