Isa ga babban shafi

Manyan kungiyoyin agaji na yi wa ECOWAS matsin lamba kan Nijar

Kungiyoyin Agaji na kasashen duniya sun bukaci kungiyar ECOWAS da ta sassauta takunkuman da ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar, sannan ta bada damar shigar da kayayyakin agajin gaggawa cikin kasar ta kan iyakar Benin. 

Shugaban Najeriya kuma shugaban ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya kuma shugaban ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Kungiyoyin kimanin 20 da suka rattaba hannu sun yi kira da a gaggauta bude kan iyakar Nijar da Benin wadda aka kulle ta sakamakon takunkuman da ECOWAS ta lafta wa kasar saboda juyin mulkin sojoji.

A wani taro da suka gudanar a ranar Lahadi da ta gabata, shugabannin kasashen na ECOWAS sun jaddada takunkuman da suka sanya wa Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a cikin watan Yulin da ya gabata.

Shugabannin na ECOWAS sun kuma bukaci mayar da mulki ga farar hula cikin kankanin lokaci kafin su sassauta wa kasar takunkuman.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ta fitar gamayyar kungiyoyin agajin da ta kunshi Oxfam da Save the Children da Medicins du Monde, ta yi kira da a bude kan iyakar Benin da Nijar domin shigar da kayayyakin jin-kai cikin gaggawa.

Sama da mutane miliyan 4 da dubu 300 ke cikin bukatar taimakon gaggawa kamar yadda kungiyoyin suka yi gargadi.

Kodayake ECOWAS ta ce, tuni ta bada izinin shigar da kayayyakin jin-kai cikin Nijar saboda talakawa, amma sojojin da ke mulkin kasar ne suka yi biris wajen kin amfani da damar da aka bayar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.