Isa ga babban shafi

ECOWAS ta amince da juyin mulki a Nijar, ta dakatar da ita daga duk hukumominta

Kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta amince da yiwuwar juyin mulki a jamhuriyar Nijar, kana kuma ta tabbatar da dakatar da kasar daga cikin ta har sai lokacin da aka mayar da kundin tsarin mulki.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da kotun daukaka kara ta umarci sojoji da su saki shugaban Bazoum
Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da kotun daukaka kara ta umarci sojoji da su saki shugaban Bazoum © KOLA SULAIMON / AFP
Talla

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan taron shugabanninta da ya gudana a birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Kafin yanzu dai kungiyar bata amince da yiwuwar juyin mulki a Nijar ba, a wajen ta wasu mutane ne kawai suka yi garkuwa da shugaban kasar Bazoum Muhammed da kuma wargaza kundin tsarin mulki.

Ta cikin sanarwar, kungiyar ta fito karara ta bayyana gamsuwa da cewa sojoji sun yiwa Bazoum juyin mulki, don haka a yanzu za’a mu’amalanci kasar ne a matsayin wadda sojoji suka kwaci mulki ta karfin tsiya.

Yayin taron, kungiyar ta bukaci sojojin su yi gaggawar mayar da mulki hannun farar hula tare da sakin shugaban kasar da suke rike da shi.

Tuni dai jagoran juyin mulkin Omar Abdourahmane Tchiani, ya yi fatali da wannan bukata, yana mai cewa babu wata kasa da zata tsarawa jamhuriyar abinda zata yi.

Ko a wata tattaunawa da Tchiani din ya yi da manema labarai a baya-bayan nan ya jadadda cewa lokaci ya yi da Nijar zata kwaci cikakken ‘yancin ta, don haka babu wata kasa da zata rika bata umarni yadda ta ga dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.