Isa ga babban shafi

ECOWAS ta sake shimfida sabbin ka'idoji don janyewa Nijar takunkumi

Shugabannin kungiyar ECOWAS sun sake shimfida wasu ka’idoji da suka ce ya zama dole sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su bi matukar suna bukatar kungiyar ta janye takunkumin da ta kakabawa kasar.

Taron ya gudana ne a birnin tarayyar Abuja
Taron ya gudana ne a birnin tarayyar Abuja AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Cikin ka’idojin har da bukatar ganin sojojin sun dauki hanyar mika mulki hannu farar hula.

Shugabannin na wadannan kalamai ne cikin matsayar da suka cimma a taron da suka gudanar kan halin da ake ciki a kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso a birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Shugaban majalisar kungiyar ta ECOWAS Omar Touray ya ce tawaga daga kasashen Benin, Togo da kuma Saliyo zasu sake bude wani zauren tattaunawa da gwamnatin sojin Nijar don duba yiwuwar cimma matsaya game da mika mulki hannun farar hula.

Touray ya ce ECOWAS din zata dauki matakin janye takunkumin  ko kuma barin sa ne bayan nazartar rahoton da tawagar zata gabatar bayan kamalla ganawa da gwamnatin sojin ta Nijar.

 

Abinda kadai zamu saurara don janyewa Nijar wadannan takunkumai sune sojojin su baiwa gwamnatin rikon kwarya damar karbar mulki matukar ba haka ba kuma zamu ci gaba da sanyawa kasar sabbin taukunkumai, inji Touray.

Jerin takunkuman da ECOWAS ta kakabawa jamhuriyar Nijar ya jefa jama’ar kasar cikin kunci, yunwa, rashin kudade da kuma ta’azzarar matsalar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.