Isa ga babban shafi

Kotun ECOWAS ta ba da umarnin sakin Mohamed Bazoum

A yau Juma'a ne kotun ECOWAS ta ba da umarnin sakin Mohamed Bazoum, shugaban Jamhuriyar Nijar tun bayan juyin mulkin da aka yi masa a ranar 26 ga watan Yuli, da kuma iyalansa.

Wasu daga cikin masu goyon bayan Majalisar sojin Nijar
Wasu daga cikin masu goyon bayan Majalisar sojin Nijar AFP - -
Talla

A wata sanarwa daga wannan kotu,alkalan sun umarci majalisar sojin kasar ta Nijar da ke tsare da Bazoum da ta gaggauta sakin ilahirin mutanen da ake tsare da su biyo bayan juyin mulki ba tare da wani sharadi ba tare da mayar da Shugaba Bazoum bakin aikinsa, kamar yadda alkalin kotun ya tabbatar a Abuja, watanni uku bayan gabatar da korafin shugaban kasa.

Wannan hukunci na kotu na zuwa ne a dai dai lokacin da majalisar sojin kasar Nijar a karkashin Shugabancin Abdourahamane Tiani ke iya kokarin ganin ta shawo kan kasashe a fuskar diflomasiyya, wanda ya sa Shugaban kasar  kai ziyara birnin Lome na kasar Togo.

Wasu daga cikin magoya bayan tsohon Shugaban kasar Nijar Bazoum Mohamed
Wasu daga cikin magoya bayan tsohon Shugaban kasar Nijar Bazoum Mohamed AFP - STEFANO RELLANDINI

A wata ziyara da Ministan harkokin wajen Togo ya kai Nijar ,da yake magana a gidan talabijin na kasar, ministan harkokin wajen kasar Togo, Robert Dussey, ya ce ya cimma yarjejeniya da firaministan kasar ta Nijar da aka nada Ali Mahaman Lamine Zeine da ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangare.

Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Nijar.
Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Nijar. AFP - -

"A shirye muke mu gabatar da shirin ga shugabannin kasashe masu shiga tsakani da kuma hukumar ECOWAS," in ji shi, yayin da yake magana kan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka.

A cikin watan Oktoba, shugabannin sojojin sun ba da sanarwar rage kashi 40 cikin 100 na kasafin kudin shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.