Isa ga babban shafi

Bazoum ya cika kwanaki 80 a hannun Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar

Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya cika kwanaki 80 a tsare tare da mai dakinsa da dansa tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yuli, lamarin da ya sa har yanzu makomarsa ke cikin rashin tabbas. 

A ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata ne Sojojin Nijar suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
A ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata ne Sojojin Nijar suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum. © Présidence Niamey
Talla

Bazoum, wanda aka zaba bisa tsarin dimokaradiyya don ya jagoranci kasar da ke yankin Yammacin Afrika, har zuwa yanzu ya kafe cewa ba zai sauka daga kan karagar mulki ba, inda har ya nemi mafita ta shari’a. 

Duk  da kiraye-kiraye da kasashen duniya da kungiyoyi da dama ke yi na sakinsa, sabuwar gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi kunnen uwar shegu da bukatar hakan. 

Tun bayan wannan juyin mulki ne Bazoum ya ke tsare a gidansa na cikin fadar shugaban kasar da ke binin Yamai fadar gwamnatin Nijar, tare da matarsa  Haziza da dansa Salem, kuma lauyansa dan kasar Senegal, Mohamed Seydou Diagne ya ce babu abin da ya sauya a game da halin da ya ke ciki. 

Wasu makusantan hambararren shugaban, sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP  cewa ana tsare da shi ne a yanayi na rashin wutar lantarki da wadataccen ruwan sha. 

Majiyoyin sun bayyana cewa ana kai wa shugaban abinci duk bayan kwanaki biyu ne, kana likitansa ya na ziyartarsa a kai-a-kai.

Likitan Bazoum Mohamed ya kara da cewa hambararren shugaban na cikin koshin lafiya kamar yadda maidakinsa da dansa suke, kuma zuwa ya tsaya kan bakarsa ne na kin amincewa da bukatar sojojin da suka yi juyin mulki da ke neman lallai ya sanya hannu a takardar yin murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.