Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Nijar ta kaddamar da sabon hukumar yaki da rashawa

Shugaban mulkin soji Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamne Tchiani ya rantsar da mambobin sabuwar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar COLDEF, da kuma mambobin Babbar Kotun kasa ta Cour d'Etat da ke yi wa tsoffin shugabannin kasa da manyan jami'an gwamnati shari’a.

Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Chiani. 16/09/23
Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Chiani. 16/09/23 © Presidence du Niger
Talla

Janar Abdourahamne Tiani da kansa ya halarci bukin kaddamar da sabbin jami’an, wanda kuma shine karon farko da ya bayyana a bainar jama'a a wajen fadar shugaban kasa, tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli ya da hambarar da uban gidansa Mohamed Bazoum.

A ranar 26 ga watan Yulin wannan shekara ne, Janar Tchiani ya hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum daga mulki, abin da ya sa kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ta kakaba mata takunkumai, tare da yanke hulda da wasu kasashen yamma ciki harda Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka.

Ecowas dai tun da farko ta bai wa sojoji masu juyin mulki wa'adi su mayar da Bazoum a kan mulki ko kuma ta yi amfani da karfin soja a kan kasar. Lamarin da ya haifar da zaman dar-dar sakanin Nijar da kungiyar Ecowas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.