Isa ga babban shafi

An bayar da belin 'yar jaridar Nijar da aka kama a watan Satumba

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun bada belin ‘yar jaridar nan, Samira Sabou, wadda da suka kama tun a watan Satumba, kamar yadda kungiyar ‘yan jarida ta duniya, wato Reporters sans Frontières  da lauyanta suka sanar a  jiya Laraba.

 Samira Sabou, 'yar jaridar kasar Nijar da aka bada belinta a Laraba.
Samira Sabou, 'yar jaridar kasar Nijar da aka bada belinta a Laraba. © Capture d'écran / rsf.org
Talla

Kafin a sake ta a maraicen Laraba, sai da aka tuhumi Samira Sabou da laifin taimaka wa wata babar kasa ta waje, da kuma laifin wallafa labaran da ke iya tayar da hankulan jama’a.

Lauyan Sabou, Ould Salem Saïd, ya shaida wa kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa wani alkalin kotu Majistre da ya saurari tuhume-tuhumen da ake mata ne ya bada belin ta.

A ranar 30 ga watan Satumba ne wasu jami’an 4  da ba a san ko su wanene ba, sanye da fararen kaya suka kama Sabou a gidanta da ke birnin Yamai.

An taba daure ‘yar jaridar da ke wallafa labarai a kafar intanet bayan da aka zarge ta da laifin bata suna, biyo bayan wani rahoton da ta yi a kan tsawwala kudin sayen makamai da wasu jami’an gwamnatin Nijar din suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.