Isa ga babban shafi

Algeria ta janye shiga tsakanin da ta ke a rikicin Nijar bayan juyin mulki

Algeria ta sanar da janyewa daga shiga tsakanin da ta ke yi wajen warware rikicin jamhuriyyar Nijar biyo bayan juyin mulkin da Sojoji suka yi a watan Yulin da ya gabata, shiga tsakanin da ke shirin samar da turbar kafa gwamnatin rikon kwarya gabanin gudanar da zabe.

Shugaba Abdelmadjid Tebboune na Algeria.
Shugaba Abdelmadjid Tebboune na Algeria. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Algeria ta fitar a jiya Litinin, ta yi zargin cewa jamhuriyyar Nijar, ba ta shirya zama a teburin tattaunawa don lalubo bakin zaren warware rikicin ba, dalili kenan da ya tilasta mata janyewa daga shiga tsakanin.

A cewar Algeria za ta dakatar da shiga tsakanin da ta ke har sai ta samu cikakkiyar amincewa kan ci gaba da aikin da ta faro tare da samun cikakken goyon baya daga sojojin da ke mulki na Nijar.

 Algeria, wadda ta ce tun a ranar 27 ga watan Satumban da ya gabata mahukuntan Nijar suka aike mata da wasikar amincewa da tayín da ta yi na shiga tsakanin da nufin magance rikicin kasar, ta bayyana cewa wannan amincewa ce ta sanya shugaba Abdelmadjid Tebboune aikewa da babban jami’in diflomasiyyar kasar Ahmed Attaf zuwa Yamai don tattaunawa.

Algeria ta ce dama tun a wancan lokaci ba a kai ga cimma jituwa game da tayin da ta mikawa Sojojin a matsayin mafita ga Nijar ba.

Sai kuma kwatsam ga wata sanarwar da ke nuna cewa tun farko mahukuntan na Nijar basu sahalewa makwabciyar ta su shiga tsakani wajen warware rikicin ba.

Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine, ya bayyana cewa, bai da masaniya game da amincewa Algeria shiga tsakani wajen warware rikicin na Nijar, domin shi kansa a shafukan sada zumunta ya ci karo da labarin, inda ya zargi kasar da yunkurin yawo da hankalin mahukuntan na Nijar.

Algieria dai ta mika tayin mulkin rikon kwarya na watanni 6 karkashin mulkin Sojin a Nijar, mulkin da zai gudana bisa sa’idon wani tsagi na fararen.

Fiye da watanni 2 kenan Sojoji na mulkin kasar ta Nijar tun bayan hambarar da gwamnatin Bazoum Mohamed a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabat, lamarin da ya haddasa tsamin alaka tsakanin kasar ta yammacin AFrika da makwabtanta har da uwar goyonta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.