Isa ga babban shafi

An fara zaman makokin kwanaki uku a Nijar bayan rashin sojojin 29

An fara zaman makoki da za a shafe kwanaki uku ana yi a Jamhuriyar Nijar daga wannan Talata, biyo bayan rasa rayukan sojoji 29, wadanda suka kwanta dama yayin da suke fafata wa da ‘yan ta’adda a kusa da iyakar kasar da Mali.

Wasu sojojin Jamhuriyar Nijar.
Wasu sojojin Jamhuriyar Nijar. AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Harin na ranar Litinin shi ne mafi muni da aka kai a Jamhuriyar ta Nijar tun bayan da sojoji suka karbi mulki a ranar 26 ga watan Yuli, abinda ya kawo karshen gwamnatin farar hula da tsohon shugaba Mohamed Bazoum ke jagoranta.

‘Yan ta’addan sun kai harin ne a arewa maso yammacin garin Tabatol kusa da kan iyaka da kasar Mali, inda ake fama da hare-haren mayakan da ke da alaka da kungiyar IS da kuma Al-Qaeda.

Ma’aikatar tsaron Nijar ta ce mahara sama da 100 ne suka kai farmakin, sai dai duk haka dakarun kasar sun samu nasarar kashe adadi mai yawa daga cikinsu.

Nijar ta dade tana fama da hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin Jihadi a kudu maso gabashinta, wadanda ke tsallaka mata daga Najeriya, yayin da wasu ‘yan ta’addan ke shiga kasar daga Mali da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.