Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya kashe sojojin Nijar 7 a yankin Tillaberi

Akalla Sojin Nijar 7 suka mutu a wani hari da ‘yan ta’adda suka kai yankin Tillaberi na kudu maso yammacin kasar mai fama da tashe-tashen hankula, yayinda wasu karin 5 suka sake mutuwa a hadarin mota, lokacin da su ke kokarin mayar da martanin harin kan ‘yan ta’addan.

Wasu dakarun jamhuriyar Nijar yayin atisaye a sansanin horas da su dake karkashin Amurka Flintlock dake garin Diffa.
Wasu dakarun jamhuriyar Nijar yayin atisaye a sansanin horas da su dake karkashin Amurka Flintlock dake garin Diffa. U.S. Africa Command - Spc. Zayid Ballesteros
Talla

Harin na jiya Alhamis ya zo ne a dai dai lokacin da dakarun Faransa da ke taimakawa kasar wajen yaki da ta’addanci ke shirin ficewa bisa bukatar hakan daga gwamnatin Sojin da ta kwace mulkin kasar watanni 2 da suka gabata.

Wata sanarwa dauke da sa hannun minsitan tsaron Nijar Salifou Mody ce ta tabbatar da harin inda ta ruwaito shi ya na cewa ‘yan ta’addan sun farmaki dakarun da ke fagen daga a garin Kandadji jiya Alhamis wanda ya yi sanadin mutuwar Soji 7.

A cewar ministan, wasu Sojoji 5 sun sake mutuwa a hadarin mota lokacin da suka nufaci mayar da martini kan hare-haren ‘yan ta’addan.

Sanarwar ta kuma ruwaito ministan na cewa, wasu sojoji 7 na daban kuma sun jikkata wadanda tuni aka mika s uga asibiti don karbar kulawar gaggawa.

Janar Salifou Mody ya bayyana cewa tawaga ta musamman ta fara aiki don bin diddigin maharan tare da kakkabe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.