Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Nijar ta zabtare kasafin kudin bana da kaso 40 cikin 100

Gwamnatin sojin Nijar ta zabtare adadin kudaden da aka shirya kashewa cikin kasafin kudin bana da kaso 40 cikin dari, biyo bayan matsalolin tattalin arziki da kasar da fada tun bayan juyin mulki.

Shugaban majalisar soji ta Nijar Janar Abdourahmane Tiani.
Shugaban majalisar soji ta Nijar Janar Abdourahmane Tiani. REUTERS - STRINGER
Talla

Wannan na kunshe ne ta cikin wata wasika da sojojin suka karanta a gidan talabijin na kasar.

Kafin juyin mulkin dai kasafin kudin kasar na kan CFA triliyan 3 da biliyan 29, sai dai yanzu gwamnatin sojin ta zabtare shi zuwa CFA triliyan 1 da biliyan 98, duk da dai babu karin haske kan bangarorin da ragin kudaden zai shafa.

Bangarori da dama na kasar sun fada cikin matsanacin hali, sakamakon takunkumai da kuma rufe iyakokin da wasu kasashe suka yi da jamhuriyar Nijar din.

Wannan mataki ya jefa 'yan kasar cikin rudani, a yayin da suke ganin rage kudaden zai kara jefa su cikin matsanancin halin da suka fada a sakamakon juyin mulki, to amma gwamnatin sojin ta ce bata da wani zabi da ya wuce hakan.

Baya ga matsalar tsaro da matsin tattalin arziki, juyin mulkin na Nijar ya jefa kasar cikin rashin tabbas, jerin takunkumai da kuma gurbacewar alaka tsakanin ta da makwaftan ta, abinda ya shafi talalawan kasar kai tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.