Isa ga babban shafi
MATSALAR TSARO

Ƴan bindiga sun sake kashe mutane a Kaduna

Najeriya – Akalla mutane 23 ƴan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai ƙauyen anguwar Danko da ke mazabar Kakangi a karamar hukumar Birnin Gwari ta Jahar Kaduna.

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba
Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba Information Nigeria
Talla

Mazauna garin sun bayyana cewar a lokacin harin, maharan sun ci karansu babu babbaka a ƙauyen da ke da nisan kilomita 10 daga cikin garin Dogon Dawa.

Ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Kakangi a majalisar dokokin jahar Kaduna Yahaya Musa Dan Salio, ya tabbatar da mutuwar mutane 23 sannan ya ce akwai wasu mutum biyar da suka samu raunuka.

Dan majalisar ya kuma tabbatar da cewar akwai wasu daga cikin mutanen garin da suka kubuto a hannun ‘yan bindigar da suka yi garguwa da su.

Sakataren yada labarai na shugaban ƙaramar hukumar ta Birnin Gwari Alhassan Ibrahim Saulawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce mutane 20 ne suka rasa ransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.