Isa ga babban shafi

Kalaman El Rufa'i kan maido da tallafin mai ya sanya 'yan Najeriya muhawara

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai, ya ce gwamnatin Najeriya ta dawo da biyan tallafin man fetur ba tare da sanin 'yan kasar ba.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i. © Twitter@GovKaduna
Talla

El Rufa’i ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a garin Maiduguri, inda ya halarci wani taro kan samar da hanyoyin inganta tsarin ayyukan gwamnati a ranar Litinin.

Tuni dai kalaman tsohon gwamnan na Kaduna suka janyo cece-kuce tsakanin ‘yan Najeriya ganin yadda har yanzu farashin man fetur ɗin bai ragu ba, kamar yadda za a ji cikin rahoton da wakilinmu Bilyaminu Yusuf ya aiko mana.

01:35

Rahoto kan martanin da 'yan Najeriya suka maida dangane da maido da tallafin mai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.