Isa ga babban shafi

EFCC tayi kokarin kama tsohon gwamnan Kogi Yahya Bello

Najeriya – Yunkurin hukumar EFCC dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na kama tsohon gwanan jihar Kogi, Yahya Bello yau a Abuja, yaci tura, sakamakon rahotannin fitar da shi daga gidansa da jami'an tsaro suka yiwa kawanya.

Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. © EFCC
Talla

Rahotanni sun ce anyi ta jin karar harbe harbe a unguwar da Bello ke zama, abinda ya jefa fargaba da kuma tsoro a tsakanin jama'a.

Shaidun gani da ido sun ce, bayan daukar dogon lokaci suna fakon Bello ya fito daga gidan, gwamna mai ci Usman Ododo ya ziyarci gidan inda ya fitar da wanda ya gada.

Bayanai sun ce, fitowar Ododo daga gidan, jami'an EFCC da tarin 'yan sanda da DSS da suka je domin kama tsohon gwamnan sun yi ta harbi sama bayan zargin cewar gwamnan ya fice da Bello daga gidan.

Wadannan harbe harbe sun razana mazauna unguwar da masu wucewa, inda suka dinga shekawa da gudu domin kaucewa harsasan dake fita.

Daga cikin wadanda suka sheka da gudu harda 'yan jaridu da magoya bayan tsohon gwamnan da kuma 'yan kallo.

Rahotanni sun ce bayan kura ta lafa, jami'an tsaron sun haura takalman su inda suka bar gidan ba tare da kama Yahya Bello ba.

Kakakin hukumar EFCC Dele Oyewale bai yi wani karin haske a kan lamarin ba, amma rahotanni sun ce an dauki lokaci ana wasan buya tsakanin tsohon gwamnan da jami'an hukumar saboda zargin da ake masa na karkata akalar kudaden jama'ar Kogi da suka kai naira biliyan 84.

Watanni biyu da suka gabata, Bello ya kammala wa'adin mulkin shekaru 8 a matsayin gwamnan Kogi, yayin da ya mika ragamar mulki ga Usman Ododo, wanda ya samu nasarar zaben da aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.