Isa ga babban shafi

Ƴan matan Chibok 21 sun dawo da yara 34

Shekaru 10 bayan sace ‘yan mata 276 da aka yi a makarantar sakandiren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno, wani rahoto da kungiyar MMF a Najeriya ta fitar, ya nuna cewa 21 daga cikin ‘yan matan da aka sako sun dawo ne da yara 34, wanda hakan ya tabbatar da cewa Boko Haram ta jima tana cin zarafin yara mata a kasar.

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka shaki iskar 'yanci da gwamnatin Najeriya ta karbe su a Abuja, ranar 8 ga watan Mayu, 2017.
Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka shaki iskar 'yanci da gwamnatin Najeriya ta karbe su a Abuja, ranar 8 ga watan Mayu, 2017. AP - Sunday Alamba
Talla

Wannan, a cewar rahoton da gidauniyar Murtala Muhammed MMF ta fitar domin tunawa da cika shekaru 10 da sace ‘yan matan, ya kasance wani mummunan al’amari da ke tabbatar da cin zarafi da auren dole da aka yi wa ‘yan matan a hannun mayakan Boko Haram.

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa iyayen wadanda aka sace 48 ne suka mutu tun daga lokacin da lamarin ya faru wanda hakan ya haifar da cikas sosai ga bangaren ilimi, da kuma makomar iyayen yara.

Shugabar gidauniyar ta MMF, Dakta Aisha Muhammed Oyebode, ta ce a cikin shekaru 10 da sace ‘yan matan Chibok da ya janyo cece-ku-ce a duniya, an gaza samar da sauyi a Najeriya inda tun daga lokacin zuwa yanzu sace-sacen dalibai ya zama ruwan dare.

Gidauniyar ta MMF, ta shawarci gwamnatin kasar da tayi dukkan mai yuwuwa wajen kawo karshen sace-sacen dalibai, musamman mata da cin zarafinsu da ake yi a sassan kasar, tare da gurfanar da duk wadanda aka samu da hannu a rikice-rikicen da ke aukuwa, ba tare da la’akari da karfin ikon su ko kuma alakarsu da gwamnati ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.