Isa ga babban shafi
Najeriya

Ga alamu Jirgin shugaban kungiyar CAN ta Kiristan Najeriya ne aka kama a Afrika ta kudu da niyyar sayen Mamai

An kama ‘yan Najeriya 2 da wani dan kasar Isra’ila 1 dauke da tsabar kudi har kusan Dalla miliyan 10 a kasar Afruka ta kudu za su sayi makamai da sunan gwamnatin tarayyar Najeriya

nigerianeye.com
Talla

Bincike da aka gudanar ya nuna cewar Jirgin da aka kama a birnin Johannesburg na Afruka ta Kudu makare da Kudi Dolar Amurka kusan Miliyan 10 na shugabban Kungiyar Kiristocin Najeriya wato CAN, Pasto Ayo Oritsejafor ne.

Yanzu haka dai wadannan mutanen na rike a hannun ‘yan sanda a kasar Afruka ta kudu, kuma wata kwakkwarra majiyar ‘yan sanda a kasar ta Afruka ta kudu ta bayyana cewar Jirgin mutanen ya tashi ne daga babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, sai dai ba’a bayyana sunayen kowanne daga cikinsu ba.

Jirgin samfurin Bombardier Challenger 600 dai matukansa 'yan Najeriya ne, kuma Captain Tunde Ojongbede ne ya tuka shi zuwa kasar ta Afruka ta kudu.

Mai magana da Yawun jami’an tsaron Afruka ta kudu Adrian Lackay ya tabbatar da cewar an gano mutanen ne bayan da aka dora kayansu akan Na’ura ta kuma nuna cewar tsabar kudi ne makare a Jikunkunan.

An kuma samu mutanen dauke da wasu Takardu da suka tabbatar cewar sun je Afruka ta kudun ne domin sayen Makamai kuma su da kansu sun tabbatar da cewar za su sayi makamai ne, kuma mai yuwa ne shi dan kasar Isra’ilar ne Dillainsu.

Hukumar samar da kudaden shiga ta kasar Afruka ta kudu dai ta karbe kudaden a filin Jirgin saman Lanseria na yankin Arewa maso yammacin birnin Jojannesburg a ranar 5 ga watan Satumba.

Hukumomi a kasar Afruka ta kudun dai sun zuba Kudaden a babban Bankin kasra har sai an kammala bincike.

Wata Jarida a kasar Afruka ta kudu City Press ta bayyana cewar mutanen da kansu sun tabbatarwa jami’an tsaron kasar cewar za su je sayen Makamai ne, sai dai an bar Jirgin ya koma babban birnin tarayya na Abuja saboda rashin amincewa da shi.

Sai dai dai daga cikin mutanen da aka kama na can tsare yanzu haka, a yayin da mutanen da ke cikin dayan jirgin da ke zaman dan rakiya ga Jirgin da aka kama, da kuma ya kwana biyu a kasar kamin zuwan na biyun da ke makare da kudi, ya koma zuwa Abuja a ran 13 ga Watan nan.

Sashen Hausa na rfi ya tuntubi mai magana da Yawun fadar shugaban kasa Mike Omeri wanda ya ce basu da labarin hakan amma za su yi bincike
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.