Isa ga babban shafi
UNICEF

Ana cin zarafin Yara kanana a Duniya-Rahoto

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da hukumar kula da Kananan Yara UNICEF ta wallafa, rahoton yace kimanin Yara Mata 120 a fadin duniya aka yi wa Fyade ko aka ci zarafinsu kafin su cika shekaru 20. Wannan kuma shi ne rahoto mafi girma da aka gudanar a kasashe 190.

Urmilla Megwal  'yar shekaru 15 da aka ci zarafinta  a kusa da 'Yar uwarta Roopa a harabar gidansu da ke kauyen Dehra jihar Rajasthan.
Urmilla Megwal 'yar shekaru 15 da aka ci zarafinta a kusa da 'Yar uwarta Roopa a harabar gidansu da ke kauyen Dehra jihar Rajasthan. UNICEF
Talla

Rahoton yace Yarinya daya a cikin 10 ake yi wa fyade a duniya. Kuma Rahoton yace kimanin Yara 95,000 aka kashe a shekara ta 2012 kawai, yawanci a kasashen Latin Amurka.

Rahoton yace yara kanana da dama ne a fadin duniya ke fuskantar gallazawa, yawanci tsakanin ‘Yan shekaru biyu zuwa 14.

Yara ‘yan tsakanin shekara 15 zuwa 19, sun fi fuskantar cin zarafi daga abokan zamansu maza ko dai kafin aure ko kuma bayan aure. Kuma wannan a cewar rahon ya fi faruwa a kasashen Afrika da suka hada da Zimbabwe da Uganda da Tanzania da Jamhuriyyar Congo.

Rahoton kuma yace Najeriya ce aka fi samun mutuwar yara kanana da ake kashewa da gangan, kamar yadda rahoton yace matsalar ta fi yawa a kasashen Latin Amurka.

Rahoton ya bayyana fargaba ga ci gaban rayuwar yara kanana saboda yawaitar cin zarafinsu da ake samu a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.