Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Vatican ta kafa kwamitin yaki da cin zarafin yara a mujami’un ta

Paparoma Francis ya kafa wani kwamiti da zai yi yaki da matsalar cin zarafin kananan yara a mujami’un katolika bayan an bashi shawarar ya yi hakan.

Fadar Vatican
Fadar Vatican REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Archbishop Sean O’Malley na kasar Amurka ne ya bayyana hakan a birnin Boston inda ya ce za a fitar da cikakken bayani game da kwamitin a nan gaba.

A jiya ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kare hakkin cin zarafin bil adama ya zargi Majalisar da kin mika bayanai game da wannan zargi.

Ana sa ran kwamitin zai fitar da dokoki ga malaman fadar, da sharuddan da za a bi a rassan cocin dake kasashen daban daban a duniya.

Matsalar cin zarafin yara a mujami’un cocin ya fara bayyana ne a kasar Amurka kusan shekaru goma da suka gabata lamarin da ya aka yi ta samun bayyanar mutanen da suka ce an ci zarafinsu musamman ma yara kanana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.