Isa ga babban shafi
Mali

Sojin Mali sun ci zarafin fararen hula-Amnesty

Kungiyar kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International, ta fitar da wani Rahoto wanda ya yi zargin an keta hakkin daruruwan fararen hula tare da cin zarafinsu da azabtar da su tun a lokacin da Dakarun Faransa suka kaddamar da yaki a kasar Mali.

Sojin Mali da ke yaki da Mayaka a Arewacin kasar
Sojin Mali da ke yaki da Mayaka a Arewacin kasar Amnesty International
Talla

A wani Rahoton bincike na kungiyar kare hakkin Bil’adama ta amnesty, kungiyar tace dakarun Mali sun ci zarafin fararen hula tare da zabtar da su.

A cikin rahoton na wata guda da kungiyar ta gudanar ta kafa hujjoji da bayanan da ta tattaro game da adadin mutanen da Sojin na Mali suka azabtar da sunan farautar Mayakan MUJAO ko Ansarudeen

Kungiyar tace ta samu zantawa da mutanen sama da 200 da yanzu haka ke fuskantar dauri akan alakarsu da Ta’addanci

A rahoton kunkiyar tace mutanen yawancinsu suna dauke da tambo daga ukubar da suka fuskanta daga dakarun na Mali

Yanzu haka kuma akwai mutane biyar da suka mutu daga cikinsu tsakanin watan Maris zuwa Afrilun bana.

A daya bangaren kuma kungiyar tace ta samu bayanan shedar kashe kashen da mayakan MUJAO suka aikata a arewacin Mali tare da zargin mayakan da keta hakkin mautane da suka hada da yi wa mata Fyade da tursasawa yara kananan rungumar makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.